Nigeria: NEMA Ta Raba Kayan Tallafi A Jihar Adamawa

HomeLabarai

Nigeria: NEMA Ta Raba Kayan Tallafi A Jihar Adamawa

Gwamnatin tarayya ta amince a kaddamar da rabiyar kayan amfani ga YH karkashin maaikatar alamuran jin kai da walwalar jama'a karkashin shugabancin Sad

Najeriya: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kafa Dokar Hana Fita A Wasu Yankuna 2
Najeriya: Za’a Fara Daukan Mahajjata 21 Ga Watan Yuli – NAHCON
Najeriya Ta Bada Hutu Ranar Talata 1 Ga Watan Mayu Don Gudanar Da Hutun Ranar Ma’aikata Na Shekarar 2018

Gwamnatin tarayya ta amince a kaddamar da rabiyar kayan amfani ga YH karkashin maaikatar alamuran jin kai da walwalar jama’a karkashin shugabancin Sadiya Umar Faruk wanda darakta janar na NEMA ze jagoranta a jihar Adamawa.

Shugaban NEMA a Yola Mr. Midala Iliya Anuhu shi ya kaddamar da rabiyar a Fofore. Ya kuma ce rabiyar ci gaban ne cikin ciyar da YH ko wani wata da sukeyi don yaye musu wahalhalu kuma yace a shirye suke suci gaba da hakan.

Yakaru Kachalla, shugaban mata na sansanin yan hijira dake Fufore a madadin sauran yan GH ta godewa gwamnatin tarayya da kuma ministan dama NEMA inda tace sun samu abinci a daidai lokaci da suke bukata tare da cewa sun gode masa kuma suna bukatar taimakon a bangaren lafiya cikin sansanin.

Shugaban gudanarwar a madadin darakta janar in ya bukaci yan gudun hijirar das u kula da matakan kare kamuwa daga COVID 19 sannan ya yi musu fatan ayi bikin babban salla lafiya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0