Najeriya: Za’a Zana Jarrabawar NECO 5 Ga Watan Octoba Zuwa 18 Ga Watan Nuwamba

HomeLabarai

Najeriya: Za’a Zana Jarrabawar NECO 5 Ga Watan Octoba Zuwa 18 Ga Watan Nuwamba

Hukumar ilimi na tarayya ta ce majalisar zana jarrabawar kamala sakandare na kasa wato NECO, ta sanar da cewa zaa fara rubuta jarabawar a ranar 5 ga w

Najjeriya: Gwamnonin Arewa Zasu Hada Kai Da Yan Sakai Don Dakile Matsalar Tsaro
Najeriya: Ali Sheriff Ya Halarci Taron Jam’iyyar APC A Maiduguri
Najeriya: Yan Kungiyar Boko Haram Sun kai Hari Kauyen Tungushe Dake Jihar Borno

Hukumar ilimi na tarayya ta ce majalisar zana jarrabawar kamala sakandare na kasa wato NECO, ta sanar da cewa zaa fara rubuta jarabawar a ranar 5 ga watan Oktoba na wannan shekara sannan a kamala shi a ranar 18 ga watan nuwanba na 2020.

Cikin sanarwa da aka fitar, Daraktan yada labarai na hukumar ilimin kasa Ben Goong, yace ministn ilimin tarayya Emeka Nwajuiba yaba da sanarwar bayan kamala taro da kungiyoyi ilimi a kasar.

Yace za.a fara rubuta jarabawar NABTEB ranar 21 ga watan satumba sannan yak are rnar 15 ga watan oktoba na wannan shekara.

Ya kara da cewa, za kuma a rubuta jarabawar shiga kolaji na NCEE a ranar 17 ga watan oktoba na wannan shekara.

Haka kuma maaikatar ilimin tace zaa rubuta jarabawar daliban sakadare na jss 3 ranar 24 ga watan agustan wannan shekara.

Kuma maaikatar tace baza ta kara lokacin d aka debe nayin rajistar NECO ba waanda zaa rufe a ranar 10 ga watan satumban wannan shekara.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0