Najeriya: Kungiyoyin ACR Da CAG Sun Wayar Da Kai Kan Canjin Yanayi

HomeLabarai

Najeriya: Kungiyoyin ACR Da CAG Sun Wayar Da Kai Kan Canjin Yanayi

Kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu na African Climate Reporters and Climate Action Group sun yi hadin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan illar canj

Najeriya: Zaben Ekiti Alama Ce Ta Nasarar Zabe A Shekarar 2019
Najeriya: Boko Haram Sun Kai Hari Karamar Hukumar Monguno
Kungiyar Nelefa Mada Ta Ziyarci Gidan Rediyon Dandal Kura

Kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu na African Climate Reporters and Climate Action Group sun yi hadin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan illar canjin yanayi da yadda yake gurbata muhalli da kuma hanyoyin day a kamata abi wajen dakile ambaliya.

Daraktan African Climate Reporters Nuruddeen Bello ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da Global Youth Climate Action Initiative wato Climate Action Group a Kaduna ranar Litinin.

Acewar Mr Bello wanda masani ne kan canjin yanayi ya bayyana yadda ake gurbata iska da kuma hanyoyin ruwa inda yace akwai bukatar ceto dabbobi da wasu halittun ruwa da kuma dakile gurbatarsu.

Haka nan ya jaddada cewa ya kamata a duba yadda za’a dakile matsalar canjin yanayi wanda yak e karuwa ta hanyarzafin rana, sababbi ciwuka da kuma sauran kalubale.

San nan yace ana samun karuwar sharar a kasar kuma ya kamata gwamnatin tarayya data jihohi dasu samar da kamfanonin sarrafa shara a kasar.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0