Akalla Mutane 142 Ne Suka Rasu Sakamakon Hare-Hare A Arewacin Najeriya

HomeLabarai

Akalla Mutane 142 Ne Suka Rasu Sakamakon Hare-Hare A Arewacin Najeriya

Rahotanni na nuna cewa mutane akalla 142 ne aka kashe a yankin arewa maso gabashin najeriya cikin sati daya kacal day a gabata Sannan aka yi garkuwa d

Najeriya: Kungiyoyin ACR Da CAG Sun Wayar Da Kai Kan Canjin Yanayi
Najeriya: Jamaatu Nasril Islam Ta Kalubalanci Manema Labarai Kan Shurin Da Sukayi Bayan An Kashe Musulmai a Mubi
Yan majalisar Najeriya Sun Bayyana Cewa Sun Yi Gyara A Kasafin Kudin Shekarar 2018 Don A Daidaita Yankuna A Kasar

Rahotanni na nuna cewa mutane akalla 142 ne aka kashe a yankin arewa maso gabashin najeriya cikin sati daya kacal day a gabata Sannan aka yi garkuwa da 44 a wannan lokaci da rashin tsaro ya kara tsananta a kasa.

Rahoton tsaro da kungiyar dangantakar kasashe ta fitar na cewa jihar Kaduna ne keda yawan matsalar inda aka samu rahoton isa har 6 da kuma na garkuwa sai kuma mai bi mata jihar Katsina.

Rahoton na cewa , a ranar 23 na watan juli na wannan shekara, wasu makiyaya sun kashe mutane 7 a Kajuru dake jihar Kaduna, ranar 24 ga watan sun kashe mutane 10 a KH Jemaa da Kaura na jihar sannan na ranar 18 ga watan an sace mutane 6 a Chikun, a Zangon Kataf mutane 1 ne aka kashe wanda ake zargin makiyaya da aikatawa.

Har ila yau rahoton na cewa a ranar 19 ga watan juli na wannan shekara, wasu da ake zargi makikiyaya ne sun kashe mutane 21 da sufetan yan sanda 1 a Kaura inda a wani rikici daban kuma mutane 3 suka rasa ransu.

A jihar kasina kuma, rahoton na cewa a ranar 18 ga watan juli na wannan shekara ne bomb ta ritsa da yara kanana 6 a KH Malumfashi dake Katsina, inda kuma a ranar kuma a yakar yan bindiga da sukeyi, rundunar sojojin najeriya da yan bindiga duka-duka 23 ne suka rasu a KH Jibia na jihar Katsina.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0